Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Mohammadu Buhari ya kai Ziyara Niger


Shugaba Mohammadu Buhari.

A safiyar yau ne sabon zababben shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari ya kai wata ziyarar girma ta karfafa dankon zumuncin a Niamey babban birnin janhuriyar kasar.

A ziyarar shi ta farko zuwa kasashen nahiyar Afirka, Shugaban kasa Mohammadou Issoufou ya taya shi murna ya kuma yaba da zaben da aka yi a Najeriya, yace hakan ya nuna cewa akwai demokaradiyya ingantatta.

Bugu da kari shugaba Mohammadu Issoufou ya bayyana hulda ta kud-da-kud tsakani Nijar da Najeriya ta fannin kasuwanci, makamashi da dai sauransu.

Shugaban kasar ya kara da cewa zai bada kwarin guywa ga shugaba Mohammadu Buhari domin a yaki ta’addanci, musamman na Boko haram da ya addabi kasashen Nijar, Najeriya, Chadi da Kamaru. Kuma ya yaba da abinda shugaba Buhari yace, na za a hada wata rundunar sojoji a garin Maiduguri wadda zata fatattaki ‘yan Boko haram.

Da yake jawabi, shima shugaba Mohammadu Buhari ya yaba da irin tarba da karramawar da ‘yan Nijar suka yi masa. kuma ya gode wa shugaba Mohammadu Issoufou domin irin kwarin guywar da ya bashi don ganin an shawo kan ta’addancin ‘yan boko haram dake hana walwala tsakanin kasashen hudu.

Ga Mani Sha'aibu da rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG