Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sauke Manyan Sakatarori


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sallami manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya daga mukamansu bayan ganawa da yayi da su a fadar gwamnati.

Duk da yake shugaban kasar bai bayyana dalilin sauke sakatararorin ma’aikatun gwamnatin tarayya goma sha bakwai ba, masu fashin baki sun bayyana cewa, hakan bata rasa nasaba da yunkurin shugaba Buhari na yaki da cin hanci da rashawa, kasancewa ana zargin irin wadannan sakatarorin da hada baki wajen yin rubda ciki da dukiyar talakawa.

Ana ganin sallamar manyan sakatarorin a wani yunkurin nisanta wannan gwamnatin da jami’an gwamnati da ake zargi da yiwa dokokin aikin gwamnatin karan tsaye da kuma cin karensu ba babbaka.

Gobe ne dai ake kyautata zaton shugaba Buhari zai rantsar da ministoci wadanda kawo yanzu ba a tantance ma’aikatu da za a tura su ba.

Ga bayanin wakilin Sashen Hausa a Abuja, Umar Faruk Musa

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00

XS
SM
MD
LG