Fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwar cewa shugaban kasar da takwaransa na Jordan wato Sarki Abdallah II ibn Hussein sun yi wata ganawa ta musamman a New York wajen taron koli na Majalisar Dinkin Duniya.
A ganawar tasu Shugaba Buhari ya yiwa Sarkin Jordan godiya bisa ga kyautar motocin sulke guda dari biyu da kasar Jordan ta ba Najeriya domin taimaka mata da yakin da ta keyi da 'yan ta'adda. Baicin hakan Buhari ya sake godewa Jordan bisa alkawarin da ta yi na baiwa Najeriya kayan yaki da zasu hada da jirage masu tashin angulu domin taimaka mata da yaki da kungiyar Boko Haram.
Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa ba Najeriya kadai ba har da kasashen dake makwaftaka da ita zasu ci moriyar kyautar ta Jordan.
Ganin cewa kasar Amurka da wasu kasashen duniya sun dade da baiwa Najeriya taimako jefi jefi amma har yanzu yaki da 'yan Boko Haram yaki ci yaki cinyewa har ma fargaba na karuwa a kasar, wani tsohon jamiin soji kuma mai sharhi akan al'amuran tsaro Janar Abdulrazak Umar yana mai cewa yaki iri biyu ne.
Injishi akwai yakin fito na fito wanda aka saba da yinsa. Amma yaki da 'yan ta'addan Boko Haram shi ne yakin sunkuru, wato ka shiga nan ka fita can. Shi wannan daban yake. Yakin sunkuru nada wuyar al'amari. Babu wanda zai ce shi ya iya kuma babu inda ake koyas dashi dalla dalla. Yaki ne na sa'a kuma ba shiryashi a keyi ba.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum