Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Dawo Nan Bada Dadewa Ba.


ABUJA: Buhari at ERGP Launching
ABUJA: Buhari at ERGP Launching

Ministan Matasa da wasanni na Najeriya Solomon Dalung yace shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana gab da dawo Najeriya bayan samun sauki da yake ci gaba da yi game da jinyar data kai shi Birnin London.

Dalun wanda yake ganawa da manema labarai a ofishin sa Abuja yace tabbas jikin shugaban ya samu sauki kuma ana sa ran dawowar sa don ci gaba da ayyukan daya soma.

‘’Tambayar da ake yi yaushe kuma ina aka kwana, shugaban kasar na nan da rai? Zai iya dawo bakin aiki, gaskiyar maganar it ace kamar yadda nake wannan maganar mun godewa ubangiji ALLAH zance alhamdulillahi shugaban kasar Najeriya ya samu sauki daga cutar da yake damun sa yanzu haka yana cikin shiri na dawo wa gida domin ya kama aiki kuma ya samu aiki wanda zai bashi damar ci gaba da aikin sa da kuma rikon amanar da ‘yan Najeriya suka bashi’’.

Ministan yace ‘yan majilisar sun takaita ziyarar da suke kaiwa London don kada haka ya shafi lamarin aikin gwamnati a mayar da gidan Abuja dake London tamkar fadar Aso Rock.

Da kuma aka tambayi Ministan ko an saya wa shugaban guba anan sai yace ba zaice kome ba game da wannan batu.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani.2’47

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Dawo Nan Bada Dadewa Ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG