Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya yaba da cigaban dangantaka da Amurka da Cuba suka samu


Shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Cuba Raul Castro jiya Litinin, Maris 21, 2016 a Havana babban birnin Cuba.
Shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Cuba Raul Castro jiya Litinin, Maris 21, 2016 a Havana babban birnin Cuba.

A cigaba da ziyarsa ta kwanaki uku da yake yi yanzu a Cuba shugaban Amurka Barack Obama ya yaba da irin cigaban da kasashen biyu suka samu a dangantakarsu da juna cikin 'yan watanni kadan duk da banbancinsu a mulkin dimokradiya da 'yancin bil Adam

Duk da cigaban da shugaba Obama ya ce sun samu a dangantakarsu ya amince har yanzu akwai banbanci tsakaninsu akan dimokradiya da 'yancin dan Adam. Ko shakka babu suna da sabanin ra'ayi akan mulkin dimokradiya da kare 'yancin bil Adam.

Bayan da suka yi shawarwari da gasken gaske ba tare da wata kumbiya kumbiya ba akan hanyoyin inganta dangantaka tsakaninsu Shugaban Amurka Obama da shugaban Cuba Raul Castro sun kira taron 'yan jarida inda suka yi jawabi tare da amsa tambayoyi.

Shugaba Obama yace kodayake ya fito fili ya fadawa shugaba Castro cewa Amurka zata cigaba da nanata batun 'yancin bil Adam da mulkin dimokradiya amma ba itace zata yanke shawara akan makomar kasar ba. Wannan lamari ne da ya rataya akan 'yan kasar.

A wani lamarin da ba'a saba ganin ba shugaban Cuba Raul Castro ya yadda 'yan jarida su yi masa tambayoyi. To saidai da aka yi masa tambaya akan fursinonin siyasa shugaban ya fusata. Cikin fushi yace a bayyana masa sunayen fursisnonin siyasa. Ya dage akan cewa kasar bata da fursinonin siyasa idan kuma akwai wasu a sanar dashi kafin dare za'a sakosu.

A wani lamari kuma da za'a ce alama ce ta cigaba jiya din kamfanin Western Union da otel din Marriot suka bi sawun wasu kamfanonin Amurka suka bude ofisoshinsu a Cuba tare da fadada ayyukansu. Wannan ya biyo bayan wata sanarwar da gwamnatin Obama ta bayar ne na sassauta takunkumi akan harkokin kasuwanci da cinikayya da aka kakabawa Cuban.

Ita kasar ta Cuba dai tana bin akidar kwaminisanci ne sau da kafa amma kukma zata bar Amurkawa suna kai ziyara kasar.

XS
SM
MD
LG