Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama ya ba kasar Libya wa'adi yayinda manyan kasashen duniya ke shirin daukar mataki na gaba


Shugaba Barack Obama yana jawabi a kan kasar Libya, a fadar White House.

Shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi cewa tilas ne dakarunsa su daina daukar matakin soja kan mutanen kasar

Shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi cewa tilas ne dakarunsa su daina daukar matakin soja kan mutanen kasar Libya. Da yake jawabi a fadar shugaban kasa ta White House, Mr. Obama ya sanar cewa, sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata tafi taro a birnin Paris kan Libya yau asabar domin sa ido kan matakin da za a dauka na kasa da kasa. Shugaba Obama ya yi gargadi da cewa, dubban mutane suna iya rasa rayukansu idan ba a tilastawa Mr. Gahdafi janye dakarunsa daga inda yan tawaye suke iko ba. Mr Obama ya kuma bayyana cewa, Amurka ba zata tura sojojin yaki a doron kasa zuwa Libya ba. Tun farko gwamnatin kasar Libya ta ayyana dokar dakatar da bude wuta ba tare da bata lokaci ba, ta kuma bayyana niyarta ta tattaunawa da ‘yan hamayya dake tawaye. Gwamnatin ta sanar da haka ne jiya jumma’a kwana guda bayanda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da dokar hana shawagin jirage ta sararin sama a kasar. Sai dai jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya tace Libya ta keta dokar daina bude wutar.

Susan Rice ta yi wannan zargin ne a wata hira da tashar talabijin ta CNN, yayinda dakarun Gadhafi ke kara kutsawa zuwa birgin Benghazi dake gabashin kasar. Mukaddashin ministan harkokin kasashen ketare na kasar Libya Khaled Kaim ya bayyana jiya jumma’a da yamma cewa, gwamnatin kasar bata da niyar shiga inda ‘yan tawaye suke da iko. Babbar jami’ar harkokin kasashen ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton tace taron da ya kunshi kasasahe ishirin da bakwai zai tattauna kan dakatar da bude wuta a Libya. Kasashen da suka amince da dokar hana shawagin jiragen sama a kasar Libya sun fara tura jiragen ruwa da jiragen sama a yankin baki daya.

Jakaden kasar Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Gerald Aroud ya shaidawa sashen turanci na BBC cewa, yana kyautata zaton kasashen waje zasu fara daukar matakin soja a Libya ‘yan sa’oi bayan taron kolin da za a yi yau a birnin Paris. Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Libya Moussa Koussa yace kasarshi ta amince da kudurin Mnajalisar Dinkin Duniya ne a matsayinta na memba. Kudurin ya bada izinin daukar dukan matakan da suka wajaba na kare farin kaya a Libya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG