Accessibility links

Obama Ya Halarci Taron Karrama Wadanda Aka Kashe a Fort Hood


Shugaban kasar Amurka Barack Obama da uwargidansa.

Karo na biyu kenan cikin shekaru biyar da shugaban Amurka Barack Obama ya sake komawa sansanin sojojin Fort Hood a jahar Texas a jiya Laraba domin halartar taron yin addu'o'i da karrama wadanda suka mutu a wani harbin da aka yi a wurin.

Da yake tsaye a gaban taron jama'ar da ya hada da iyalai, da abokai, da abokan aikin mutanen da suka mutu, ko suka ji ciwo a makon da ya gabata, shugaba Obama ya ce harbin da aka yi a makon jiya ya fama gyambon da har yanzu bai warke ba tun harin dubu biyu da tara da Manjo Nidal Hasan ya aikata a Fort Hood, wanda ya halaka mutane goma sha uku. A bara aka yankewa Hasan hukuncin kisa.

Mako daya kenan da gardama ta kaure da karamin soja Ivan Antonio Lopez akan hutu. Masu bincike sun ce Lopez yayi harbi kan sojojin da yake aiki da su da sauran wadanda tsautsayi ya ratsa da su ta hanyar sa a lokacin da yake harbin ba ji ba gani har tsawon mintoci takwas.

Ya kashe mutane uku, ya raunata goma sha shida kafin ya juya bindigar kan sa.

Mr.Obama ya gayawa iyalan wadanda aka kashe, dake cikin juyayi cewa babu wata kalmar da za ta isa ta raba su da bacin rai. Sannan kuma yayi alkawarin kara yin kokarin kusantar sojoji da tsofaffin sojojin da ke cikin wata damuwar da ke yi mu su illa, da kuma bayar da kulawar likitoci ga wadanda ke fama da matsalolin tabun hankali.

Masu bincike sun ce har yanzu ba su san dalilin da ya sa Lopez dan shekaru talatin da hudu ya aikata harbin ba.
XS
SM
MD
LG