Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Shekara 16 Ya Soki Dalibai 19 da Wuka


Jami'an tsaro sun kama Alex Hribal wanda ya soki 'yan uwansa dalibai da wuka
Jami'an tsaro sun kama Alex Hribal wanda ya soki 'yan uwansa dalibai da wuka

A jihar Pensylvania ta Amurka wani dalibi dan shekara 16 ya soki dalibai 'yan uwansa 19 da wuka kafin a shawo karfinsa

'Yan sandan jahar Pennsylvania sun gano kuma sun tuhumi wani yaro dan shekara 16 mai suna Alex Hribal, da ake zargi da sara da kuma sukan wasu 'yan uwan shi dalibai 19, gami da wani mai gadi daya a wata makarantar sakandare.

Bayan harin na jiya Laraba a Murrysville da ke kimanin tazarar kilomita 25 gabas da Pittsburgh, hukumomi sun ce an tuhumi Alex Hribal kamar babba da laifuffuka hudu na yunkurin neman yin kisan kai da wasu laifuffukan 21 na aikata mummunan hari.

Jami'ai sun ce Alex Hribal, dauke da wukake biyu, ya kai hari ba ji ba gani, jim kadan kafin dalibai kimanin dubu 1 da 200 su shiga azuzuwan su, su fara karatu a makarantar sakandaren Franklin Regional. Karshen ta dai wani mataimakin shugaban makarantar ne ya fi karfin yaron ya kwace wukaken daga hannun shi.

Kakakin wani babban asibiti ya ce hudu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, na cikin halin rai kwakwai, mutum kwakwai, amma ana tsammanin za su rayu. Wasu bakwai kuma na cikin hali mai tsanani da raunuka a gangar jiki, ko kirji ko a ciki ko kuma a baya.
XS
SM
MD
LG