Accessibility links

Shugaba Obama Ya Taya Mitt Romney Murnar Zama Dan Takarar Republican

  • Aliyu Imam

Shugaban Amurka Barack Obama.

Shugaba Barack Obama ya taya abokin hamayyar sa na jam’iyyar Republican Mitt Romney, sabo da nasarar da ya samu na zama mutuminda jam’iyyar Republican zata tsayar a zaben shugaban kasa.

Shugaba Barack Obama ya taya abokin hamayyar sa na jam’iyyar Republican Mitt Romney murna, sabo da nasarar da ya samu na zama mutuminda jam’iyyar Republican zata tsayar a zaben shugaban kasa.

Wani kakakin kwamitin yakin neman zabe Mr. Obama ya ce, shugaban na Amurka dan Democrat, ya tattauna da abokin takarar sa dan Republican na wani dan gajeren lokaci a safiyar laraban nan, bayan da Mr. Romney ya sami kuri’un da suka kai shi ga samun nasara a zaben d a aka yi ranar Tlata a jihar Texas.

Mr. Romney ya sami kamar kuri’un wakilai 88 cikin fiyeda kuri’ar wakilai 150 da jihar take da shi, wanda hakan yasa ya haye kuri’u 1,144 da yake bukata domin zama dan takara da jam’iyyar zata tsayar a zaben kasa na bana.

Ta bakin kakakin kwamitin yakin neman zaben Mr. Obama, shugaban ya gayawa Mr. Romney cewa yana “fatan ganin lokacinda zasu tafka muhawara sahihi kan makomar Amurka”.

Kwamitin yakin neman zaben Mr. Romney yace tattaunawar da suka yi ba mai tsawo bace, amma cikin mutunci da walwala.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG