Accessibility links

Shugaba Obama zai gana da dangin wadanda aka kashe a Colorado


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama zai tafi jihar Colorado domin ganawa da dangin wadanda aka harbe a harin da aka kai a wani gidan silma

Shugaban Amurka Barack Obama zai tafi jihar Colorado yau domin ganawa da dangin wadanda aka harbe a harin da aka kai a wani gidan silma ranar Jumma’a da asuba da ya yayi sanadin kashe mutane 12 da dama kuma suka raunata.

Jiya asabar kwararru a fannin boma bomai suka warware dukan manyan nakiyoyi kimanin sittin a gidan mutumin da ake zargi da kai harin dake kusa da birnin Denver.

Babban jami’in ‘yansanda na Aurora Dan Oates yace an harke gidan da nakiya da nufin kashe wanda ya fara shiga ciki. Bisa ga cewarshi, ba zai wuce jami’in dansanda ba.

Jami’ai sun ce James Holmes wani dan shekaru 24 da ya kamala karatun jami’a, ya yi ruwan harsasahi a gidan silman dake shake da jama’a.

An kama Holmes a harabar gidan silman jim kadan bayan harbe- harben yana dauke da bindigogi uku da kuma na’urar kare fuska daga shakar iskar gas da kuma rigar kariyar harbin bindiga. Yanzu haka ana tsare da shi a wani wuri a kadaice.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG