Accessibility links

Shugaba Omar al-Bashar na kasar Sudan, yayi barazanar ayyana yaki kan Sudan ta kudu

  • Steven Ferri

Shugaba Omar al-Bashar na kasar Sudan.

Ganin yadda ake ci gaba da fafatawa tsakanin sojin Gwamnatin Sudan da na Sudan ta kudu, shugaba Omar al-Bashar na kasar Sudan yayi barazanar ayyana yaki kan Sudan ta kudun domin kece raini kan yankin kan iyakaar da suke jayayya kansa.

Wani jawabin da ya yiwa taron magaoya bayan Gwamnatinsa yau Alhamis a Sudan, shugaba al-Bashir yace yanzu ya zama wajibi a koyawa Kudancin Sudan wani darasi ta hanyar amafani da kaarfin soja, don haka ya rantse cewar sai sojin Sudan sun sake kwato garin nan mai albarkatun mai na Heglig da sojin kudancin Sudan ke mamaye dashi a yanzu.

XS
SM
MD
LG