Accessibility links

Sudan da Sudan ta kudu suna son kaucewa barkewar yaki

  • Jummai Ali

Sojojin kungiyar SPLA kusa da fagen dagan Heglig.

Amirka tace Sudan d Sudan ta kudu suna son samun hanyoyin barkewar yaki gadan gadan tsakaninsu.

Amirka tace kasashen Sudan da Sudan ta kudu suna neman hanyar hana barkewar yaki gadan gadan a tsakaninsu, a yayinda ake ci gaba da fafatawa akan iyakar kasashen biyu.

Bayan tattaunawa da jami'an bangarorin biyu, wakili Amirka na musamman a Sudan Princeton Lyman ya fadawa 'yan jarida a jiya Alhamis cewa, galibi duk bangaren da yayi wa magana, sai suce sufa basa kaunar barkewar yaki tsakaninsu. Suna bukatar samun mafita.

Mr. Lyman yace Sudan ta kudu tana sun tabbaci kafin ta janye daga Heglig, cewa yan yakin sa kai wadanda Sudan ke marawa baya ba zasu kara kai hare hare ba, sa'anan kuma Sudan ta janye sojojinta daga birnin Bayei.

Mr. Lyman yace Sudan ta yi na'am da wannan shiri amma bisa ka'ida.

Jiya Alhamis baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace, mamaye Heglig da Sudan ta kudu tayi a makon jiya, ya keta diyaucin kasar Sudan makwapciyarta. A saboda haka ya bukaci Sudan ta kudu data janye sojojinta daga yankin na kan iyaka mai arzikin mai, yankin da dukkan kasashen ke ikirarin cewa malakinsu ne,

Haka kuma Mr Ban yayi kira ga Sudan data kawo karshen hare haren da take kaiwa yankunan Sudan ta kudu, kuma ta janye sojojinta daga yankin Abyei da ake rikici akansa.

Kasashen biyu su kasa magance rikici ku kuma sabanin akan iyakokinsu da albarkar mai da kuma wasu batutuwan da suka kunno kai bayan Sudan ta kudu ta samu 'yancinta. Masu shiga tsakanin na kungiyar kasashen Afrika suma sunyi kokarin agazawa bangarori magance batutuwansu amma nasara kalilan wannan yunkuri ya samu..

XS
SM
MD
LG