Wannan ce ziyarar shugaban Amurka Donald Trump ta farko zuwa wani yanki da ake yaki a matsayin shugaban kasa, kuma kusan a sirrance ya yi wannan tafiyar.
“Ban dade da dawowa daga ziyartar dakarun Amurka da ke Iraqi da Jamus ba,” abin da Trump ya rubuta kenan a shafinsa na twitter bayan da ya isa gida. Ya kuma ce “abu daya da na tabbatar da shi shine, muna da mutanen da ke wakiltar kasarmu, mutanen da suka san yadda ake cin nasara.”
A daren ranar Kirsimeti ne Trump da uwar gidansa Melania suka bar Washington don su kai wa dakaru, da manyan jami’an sojan Amurka ziyara, su kuma gode musu akan aikin da suke yi, da nasarorin da suka samu, da kuma sadaukar da ran da suka yi, bayan haka su yi masu barka da Kirsimeti.”
Abunda sakatariyar yada labaran fadar White House Sarah Sanders ta rubuta a shafinta na twitter a jiya Laraba da rana kenan.
A lokacin da yake yi wa dakarun jawabi, Trump ya kare matakinsa na janye dakarun Amurka daga Siriya, yana mai cewa an karyawa ‘yan ISIS laggo kuma an ruguza daularsu.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum