Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Bukaci Mekziko Ta Hana Bakin Hauren Ratsa Kasarta


 Wasu bakin haure da jami'an tsaron Amurka su ka tsayar
Wasu bakin haure da jami'an tsaron Amurka su ka tsayar

A cigaba da murza gashin bakin da ake yi tsakanin Amurka da kasar Mekziko saboda zargin barin bakin haure da ratsawa da kasar zuwa cikin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce Mekziko ta hana bakin hauren ko kuma a sake lale.

A jiya lahadi gwamnatin Trump ta bukaci Mexico da wasu kasashe uku na tsakiyar Nahiyar Amurka da su hana kwararowar dubban bakin haure da ke dosar Amurka, ta na mai nuni da cewa hatta tsohon Sakartaran harkokin cikin gida a gwamnatin shugaba Barack Obama da ta shude ya amince akwai matsalar bakin haure a iyakar Amurka da ke kudu.

“Mu na bukatar taimakonku,” abin da mukaddashin shugaban ma’aikatan fadar White House, Mick Mulvaney, ya fada wa Mexico, Guatemala, Honduras, da kuma El Salvador kenan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ABC News. Ya ce ya kamata Mexico ta dada inganta tsaron kan iyakarta da Guatemala da ke sashin kudu don ta hana bakin haure da suke tafiya zuwa arewa su shigo Mexico zuwa Amurka da kuma cewa kasashe uku na tsakiyar nahiyar Amurka bukatar hana ‘yan gudun hijira barin kasashen nasu.

Ya bar kofa a bude da yiwuwar cewa shugaba Donald Trump zai rufe kan iyakar Amurka tare da Mexico a cikin kwanaki masu zuwa, kamar yadda ya ce yana da niyar yanke kusan dala miliyan 500 a taimakon da Amurka take baiwa kasashe uku na Northern Triangle

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG