Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Ce Bai San Makomar Ganawarsa Da Shugaban Koriya ta Arewa Ba


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Duk da cewa Koriya ta Arewa ta takaita ayyukan makaman nukiliyarta da zummar yin watsi da shirin gaba daya har yanzu shugaban Amurka Donald Trump na cewa babu tabbasa akan makomar taron.

Shugaba Trump na Amurka jiya Lahadi yace, babu abunda Amurka ta rasa, ko ta bayar gabannin taron kolin da zai yi tareda shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un, yayinda ita kuma Korya ta Arewan tuni ta takaita ayyukan habaka makaman Nukiliyarta.

Duk da haka shugaba Trump ya yarda cewa babu tabbas kam makomar shawarwari da zai yi da shugaba kim. Har zuwa yanzu hukumomin kasar da suke Pyonyang basu amince, su wargaza makaman kare dangi da suka tara, kuma duk da ikirarin da shugaba Trump yake yi, kasar bata amince da kawar da makaman Nukiliya a mashigin kasashen korea guda biyu har abada ba.

Koriya ta Kudu tace, Koriya ta Arewa ta nuna sha'awar kawar da makaman Nukiliyarta baki daya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG