Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Janye 'Yancin Sojoji Na Sauya Jinsi


Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya soke tsarin da ya ba sojoji damar sauya jinsinsu na asali yayinda suke aikin soja

Shugaba Donald Trump yace yanzu rudunar sojan kasar ba zata bari wadanda suka sauya jinsinsu na asali su yi aikin soja a kowanne mataki ba, abinda ya sauya tsarin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Barack Obama ta sanar bara.

A jerin bayanai da ya yi ta hanyar sadarwar twitter, Trump yace, “bayan na nemi shawarar jami’an soja da kuma kwararru na a fannin aikin soja”, zan daina amincewa da wadanda suka canza jinsinsu suyi aiki a rundunar sojojin kasar.

Ya rubuta cewa “tilas ne rundunar sojinmu ta maida hankali kan samun gagarumar nasara, ba za a dora mata nawayar tsadar jinyar da masu canza jinsi suke jawowa rundunar ba. Na gode" in ji shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG