Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Karbi Bakuncin Prime Ministan Thailand


GOP 2016 Convention
GOP 2016 Convention

Prime ministan Thailand ya kawo ziyara a fadar white House kma sun tattauna da shugaba Donald TRump

Prime Ministan Thailand ya kawo ziyara a fadar White House, wanda wannan wata karramawa ce ga shugaba na soja ne da yayi juyin mulki a shekarar 2014, kuma kememe yaki mika mulki ga farar hula.

Yanzu haka dai Shugaba Trump da matarsa sun karbi bakuncin Prayuth Chan Ocha shi da matar sa a white House inda shugabanni suka tattauna.

Ganawar ta shugaba Trump da Prayuth tana zuwa ne kwana daya bayan da kotun kasar a Thailand ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga tsohuwar Prime Ministan kasar Yinluck Shinawatra, saboda samunta da laifin yin sakaci da aiki.

Kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama dama Amurka sun soki gwamnatin sojan ta kasar ta Thailand saboda juyin mulkin, suna zargin matakin ya janyo take hakkin Bil’adama da ‘yancin Demokuradiyya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG