Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Nada Christopher Wray A Matsayin Shugaban Hukumar FBI


A yau Laraba Shugaban Amurka Donald Trumnp ya bayyana tsohon mai shigar da kara Christoper Wray a matsayin wanda zai maye gurbin shugaban hukumar bincike ta FBI, wato James Comey.

Sanarwar da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na twitte, na zuwa ne kwana guda kafin Comey, wanda Trump ya kora a aiki a watan da ya gabata, ke shirin bayyana a gaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar Dattawa domin ba da bahasi.


Ana sa ran za a yi mai tambayoyi kan zargin cewa Trump ya yi yunkurin hana shi gudanar da bincike kan zargin cewa a gangamin yakin neman zaben shi shugaba Trump, ya hada kai da kasar Rasha.

Shi dai zabin na Trump, wato Wray, ya taba shugabantar sashen dake kula da hukunta manyan laifuka daga shekarar 2003 zuwa 2005 a lokacin zamanin tsohon shugaban Amurka, George W. Bush.


Yanzu haka yana aiki ne a wani kamfanin hadakar lauyoyi na King and Spalding mai zaman kansa, inda yake rike da matsayin mai kare wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG