Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Sanya Hannu a Dokar Rage Farashen Magunguna


Shugaban Amurka Donald Trump

Ranar Juma’a 24 ga watan Yuli Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a wasu dokokin Shugaban kasa guda hudu da zimmar rage kudaden da Amurkawa ke kashewa kan magungunan da likitoci ke rubuta musu, a yayin da ya ke fuskantar gwagwarmayar neman sake cin zabe da kuma caccaka akan yadda ya tunkari annobar COVID-19 a kasar.

Da ma a baya Trump ya ce zai yi kusan dukkan sauye sauyen da dokar wadda ya sanya wa hannu a ranar Juma’a ta kawo, amma wannan ne karon farko da aka sanya wa dokar hannu.

Daya daga cikin dokokin za ta bada dama a shigo da magungunan da likitoci ke rubutawa masu rahusa daga kasashe kamar Canada a hukumance, yayin da wata dokar kuma za ta bukaci kamfanonin da ke sarrafa magunguna su rage farashensu, a cewar Trump.

Wata dokar kuma na bukatar a rage farashen allurar insulin yayin da doka ta hudu, wadda ta yiwu ba za a aiwatar da ita ba idan aka samu nasara a ganawar da ake da kamfanonin magunguna, za ta bukaci tsarin Inshorar Medicare ya sayi magunguna a farashen da sauran kasashe ke saye, a cewar Trump.

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG