Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Dauki Kwararan Matakai Kan Shige da Fice da Kiwon Lafiya


Shugaba Trump a taron gwamnonin jihohin Amurka
Shugaba Trump a taron gwamnonin jihohin Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin daukar kwararan matakai kan harkokin shige da fice, da kiwon lafiya.

Sai dai zai bukaci taimako daga shugabannin jihohin kasar wajen aiwatar da tsare tsaren. Shugaban Amurka ya yi magana da gwamnoni a wajen taronsu na shekara shekara da aka gudanar jiya Lahadi a nan Washington DC inda ya nemi jin ra’ayoyinsu kan yadda ya kamata fadar White House ta tunkari batutuwan. Mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya yi masu karin bayani

Dangane da batun shige da fice, shugabannin daga dukan jam’iyun sun bayyana kalubalar dake tattare da tsarin da ya zama da sarkakiya da kuma wahalar gyarawa. Gwamnan jihar Utah Gary Herber da takwaransa na jihar Virginia, Terry McAuliffe sun bayyana shakkunsu da matayinsu

Yau Litinin ne ake kyautata zaton gwamnonin jihohin zasu bayyana tsare tsarensu a wani zama da za a yi a fadar White House tare da shugabannin majalisun tarayya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG