Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama da Firai Ministan Birtaniya David Cameron sun ce tilas ne Gadhafi ya sauka daga karagar mulki


Firai Ministan Birtaniya David Cameron da shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama da PM Ingila David Cameron sun ce za’a ci gaba da daukan matakan soji a Libya,har sai shugaba Moammar Gadhafi ya daina kai hari kan farar hula kuma yayi murabus..

Shugaban Amurka Barack Obama da Pirai Ministan Ingila David Cameron sun ce za’a ci gaba da daukan matakan soji a Libya, har sai shugaba Moammar Gadhafi ya daina kai hari kan farar hula kuma yayi murabus. Da suke magana laraban nan a taron hadin guiwa da manema labarai a Ingila, shugaba Obama yace ba za’a yi sassauci kan matsin lamba da suke yi wa Gadhafi ba. Mr. Cameron yace Ingila zata yi amfani da duk wata kafa ta kara matsin lamba kan Gadhafi. Duka shugabannin biyu sun ce burinsu shine baiwa ‘yan kasar Libya damar shata makomarsu. Shugaba Obama yace ya hakikance kungiyar tsaro ta NATO zata sami nasara kan dakarun Gadhafi, amma yace hakan sai samu ne “sannu a hankali.” Shugaba Obama yace Amurka da tarayyar Turai zasu ci gaba da matsin lamba kan shugaba Bashar al-Assad na Syria, wanda dakarunsa suke ta kaiwa masu zanga zangar kin jinin gwamnati hari. A taron kolin kasashe masu arzikin masana’antu da za’a yi makon nan a Faransa PM. Cameron yace shi da shugaba Obama zasu nemi taron manyan kasashe masu arzikin masana'ntu da za a gudanar ya aiwatar da wani gagarumar shirin tallafin tattalin arziki da siyasa ga kasashe dake gabas ta tsakiya da arewacin Afirka da suka rungumi canji. Shugaban Ingilan yace shi da shugaba Obama sun amince zasu ci gaba da tallafawa wadanda suke fafutukar neman ‘yanci.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG