Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Janye Tabbaci Kan Yarjajjeniyar Nukiliyar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump.

Kamar yadda aka yi hasashe a baya, yarjajjeniyar nukiliyar Iran ta fara tangal-tangal, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ki tabbatar da sahihancinta jiya Jumma'a. A gefe guda kuma Iran na barazanar maida martani mai tsauri.

Jiya Jumma'a, bayan da Shugaba Donald Trump ya ce Iran ba ta kiyaye lamirin yarjajjeniyar da ta rattaba hannu a kai da manyan kasashen duniya, sai ya bayyana wasu matakai masu tsauri da zai gindaya ma ta, ciki har karin takunkumi da zummar dakile niyyar gwamnatin Iran ta kirkiro makaman nukilya.

"Yau, ina mai shelar wasu matakanmu da wasu hanyoyi dabam-dabam da za mu yi amfani da su wajen tinkarar take-taken takala na gwamnatin Iran; kuma saboda mu ga cewa har abada - hakika, I na nufin har abada - Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba," a cewar Trump a wani jawabinsa da aka yada daga Fadar White House ga kasa baki daya, ta gidan talabijin.

Hasali ma, kiris ya rage ya tsame Amurka daga yarjejjeniyar ta 2015 da aka cimma tsakanin Iran, da kasashe masu kujerun dindindin a MDD da Jamus da kungiyar Tarayyar Turai. To amma ya ce ba zai kara bayar da tabbaci kan salon Iran wajen kiyaye yarjajjeniyar ba, wanda ke nufin ya baiwa Majalisar Tarayyar Amurka kwanaki 60 ta yanke shawara kan ko da bukatar a dau wasu matakai na gaba.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammed Javad Zarif, ranar Laraba ya yi barazanar abin da ya kira, "martani mai tsanani" muddun Trump ya ayyana Iran a matsayin marar kiyaye yarjajjeniyar. Wani mai magana da yawun rundunar sojin Iran kuma ya kara da cewa idan ta kama, sojojin kasar za su koya ma Amurka darasi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG