Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Na Shirin Kiran Iyalan Sojojin da Aka Kashe a Nijar


Shugaban Amurka Donald Trump a taron manema labarai jiya a Fadarsa ta White House

Bayan manema labarai sun tambayeshi dalin da bai kira iyalan sojojin Amurka da aka kashe a Nijar ba sai Shugaba Trump yace yana shirin yin hakan amma ya kara da cewa shugabannin baya da suka hada da Barack Obama basa kiran iyalan sojojin da suka mutu bakin aikin, kalamun da nan take aka karyata

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya ce yana shirin kiran iyalan sojojin Amurka hudu da aka kashe a farkon watannan a Jamhuriyar Nijar, ya kuma yi tutiyar cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama baya kiran iyalan sojojin da aka kashe a bakin aiki domin yi musu ta’aziyya.

Trump dai yayi wannan furuci ne a lokacin taron manema labarai a fadarsa ta White House jiya Litinin, inda aka tambaye shi dalilin da yasa bai yiwa Amurkawa wani bayani ba akan sojojin Amurka da aka kashe a Nijar.

Shugaban dai ya ce ya rubuta wasiku na musamman ga iyalan sojojin, kuma yana shirin kiransu ta wayar talhodon jajanta musu.

Ya ci gaba da cewa “yadda aka saba a baya shine, idan ka kalli shugaba Obama da sauran shugabannin kasa da aka yi a can baya, yawancinsu basa kiran irin wadanan iyalin sojojin ta waya.”

Sai dai kuma tshohuwar mataimakiyar shguaban ma’aikatan Obama, Alyssa Mastromonaco, ta mayar da martani ga kalaman Trump ta shafin Twitter, inda ta karyata maganar Trump.

Da aka sake tambayar shugaba Trump ya kara bayani kan wannan zargi da yayiwa Obama, Trump ya ce abin da aka fada masa kenan.

A farkon watan nan ne ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta fitar da sanarwar cewa an kashe sojojin Amurka na musamman guda hudu da ake yiwa lakabi da Green Berets a Nijar, a yayin wani sintirin hadin gwiwa da takwarorinsu na Nijar, inda ita ma Nijar aka kasha mata nata jami’an tsaro guda hudu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG