Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Trump Ya Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan.


Shugaban Amurka Donald Trump

A madadin Amurka da uwargidansa Melania, shugaban Amurka Donald Trump ya taya musulman Amurka murnar tsayawar watan azumi tare da yi masu fatan alheri samun albarkar watan Ramadan

Bayan an bayyana ganin watan azumin rammadan, wanda ke umurta musulman Amurka dama na duniya baki daya yin azumi, ina mika fatan alheri na ga Musulman Amurka dama na duniya baki daya.

Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa "A wannan watan, Musulmai a fadin duniya suna kara kusantar mahaliccin su ne ta gudanar da azumi, yin sadaka, karatun Kur’ani, da dai wasu harkokin ibada. musamman ma da yake a cikin wannan watanm ne aka saukar da Kur’ani mai tsarki ga Annabi Muhammadu Tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi."

Shugaba Trump ya ce watan azumin Ramadan lokaci ne da aka san musulmai da duba inda suka fito da kuma inda suke da kuma inda suka dosa a cikin addinin su domin yiwa ALLAH subuhanahu wata’ala godiya na irin ni’imar da yayi musu.

Yace fata a nan shine a cikin irin wannan lokaci ga masu azumi, akwai bukatar su karfafa zamantakewa tsakanin su da mutanen da suke zaune dasu kana su taimaki mabukata, tare da bada kyakkyawar gudummawa yadda ya dace ayi rayuwa mai albarka.

Shugaba Trump ya ce lokacin watan azumi yana tunatar damu yadda musulmai masu hannu da shuni na Amurka ke taimakawa rayuwar Amurkawa masu karamin karfi.

Ya ce mu anan Amurka munyi sa’ar samun kanmu cikin tsarin mulkin dake baiwa kowane dan kasa damar gudanar da ko wane irin ibada ya zaba yayi ba tare da tsangwama ba.

Dokar ta baiwa dukkan musulmai daman gudanar da azumin watan ramadan yadda addinin su ya bukace su su yi, ta yin hakan ne dokar kasa kuma ya bada bayanan yadda dukkan Amurkawa zasu kara fahimtar muhimmacin ranar

Daga karshe ni da mai daki na Melania muna yi maku fatan wata mai albarka. Ramadan Mubarak

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG