Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Isa Birnin Paris Domin Halartar Taro Akan Canjin Yanayi


Shugaba Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, ya isa birnin Paris a yammacin jiya Lahadi, yayin da kasashen duniya manya da kanana, masu arziki da marasa arziki, suka hallara domin tattaunawa kan yadda za a kare gurbata mahalli.

A cewar Obama: “abinda ya banbanta a wannan taro da sauran, shi ne fiye da kasashe 180, tuni sun gabatar da tsare-tsarensu kan yadda za a rage hayakin da ke haddasa sauyin yanayi, kuma Amurka na kan gaba wajen ganin an cimma wannan buri.”

A wani sako da shugaba Obama, ya fitar a shafin sada zumunci na Facebook a jiya Lahadin, shugaban na Amurka, ya nuna kwarin gwiwar cewa za a kai ga gaci a wannan taro da za a fara a babban birnin Faransa.

Burin wannan taro dai shi ne a san yadda za a rage dumamar yanayi zuwa maki biyu na degree Celcius, ko kuma ma kasa da haka, ta hanyar dakile yawan fitar da hayakin da ake dangantawa da haifar da dumamar yanayin.

Sai dai wasu na ganin akwai damuwar ko za a iya samun hadin kan kasashen baki daya a wannan taro, idan aka yi la’akkari da yadda aka samu rarrabuwar kawuna a shekarar 2009 a birnin Copehangen tsakanin kasashe masu arziki da marasa arziki.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG