Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Nemi Izinin 'Yan Majalisa Ya Yaki Kungiyar ISIS


Shugaban Amurka Barack Obama

A wani sabon yunkurin kawar da barazanar kungiyar ISIS Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi izinin tura dakarun kasar zuwa yakar kungiyar.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga majalisar kasar jiya Laraba, da ta bada izini a hukumance na amfani da karfin soja a yaki kungiyar ta’addanci mai da’awar jihadi, wato ISIS da ta mamaye wasu yankunankasashen Syria da Iraqi.

Da yake Magana, Mr Obama yace bukatar da ya gabatar ba neman yakin kuntumbala ba ne irin wanda Amurka tayi a Iraq da Afghanistan.

Shugaba Obama ya bayyana cewa izinin zai bashi damar tura dakaru na musamman idan Amurka ta sami bayanan leken asiri misali kan inda shugabannin kungiyar ISIS suke taro.

Izinin da ake nema na tsawon shekaru uku kuma ya haramtawa dakarun yin yaki gadan gadan akasashen.

“Wannan wani aiki ne mawuyaci, kuma zai ci gaba da kasancewa mawuyaci na lokaci mai tsawo”, inji shugaba Obama a wani bayani da yayi da aka yayata a tasoshin talabijin. “Amma dakarunmu suna kai hari amma Kungiyar ISIL tana kare kanta. Duk da haka ba zata yi nasara ba”.

Tsarin da shugaba Obama ya gabatar ya bayyana cewa, za’a bar yakin kuntumbala irin wanda aka kai a Iraq da kuma Afghanistan ga dakarun kasar a maimakon rundunar sojin Amurka.

Shirin zai soke matakin da aka dauka a shekara ta dubu biyu da biyu da ya bada umarnin yakin Iraq amma za’a bar izinin shekara ta dubu biyu da daya da aka bada jim kadan bayan kai hare haren sha daya ga Satumba na kamfen kan al-Qaida da abokan kawancenta.

XS
SM
MD
LG