Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Yiwa Amurkawa Jawabin Ban Kwana Jiya


Shugaba Barack Obama yayi jawabin ban kwana jiya

Jiya Talata da dare, shugaba Barack Obama na Amirka ya gabatar da jawabin ban kwana ga Amerikawa a yayinda yake shirye shiryen sauka daga kan ragamar mulki.

A yayinda yake gabatar da jawabi a garinsu Chicago a gaban dubban mutane wadanda suka yi ta kururuta cewa suna son yayi mulki wasu karin shekaru hudu, shugaba Obama yace yana son yayi godiya ga zantawar da yayi da mutane, zantawar da ya ce sun kara masa karfin gwiwar jan ragamar mulki

Shugaba Obama ya bayyana irin abubuwan da gwamnatin sa tayi cikin shekaru takwas da suka shige, ciki harda farfado da tattalin arzikin Amirka da kashe Osama Bin Laden da kuma ganin cewa Iran ta dakatar da shirin nukiliyar ta.

Bayan shi kansa,a madadin matarsa Michele, ya godewa wadanda cikin makoni biyu da suka shige suka yi ta aika masa sakonin fatar alheri bayan ya sauka daga kan karagar

Shugaban ya kammala jawabinsa da kalmomi guda uku da yayi amfani dasu a lokacinda ya fara yakin neman zaben shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da takwas—YES WE CAN, ma’ana E zamu iya yi.

XS
SM
MD
LG