Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Zafafa A Cecekucen Cinikayya da Kasar China


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Da alama tsugune bata kare ba tsakanin Amurka da China saboda shugaban Amurka ya kara saka harajin dala biliyan 100 akan wasu kayayyakin China

A wata sabuwa kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya kara zafafa a cecekucen cinikayya da Chana, inda ya umarci hukumar cinikayyar Amurka ta kara kudin haraji na dala biliyon 100 a kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su daga Chanan.


Wannan matakin ya zo ne kwana daya bayan da Chana ta yi karin haraji a kan wasu kayayyakin Amurka, kamar waken soya da kananan jiragen sama da kudn su ya kai dala biliyon 50. Martanin na Beijing ya biyo bayan haraji da Amurka ta dorawa wasu kayayyakinta dake shiga Amurka da dala biliyon 50 a farkon wannan mako.


Kasuwar hannu jari a Amurka ta yi kasa biyo bayan umarnin da Trump na baya bayan nan. Hannayen jari a kasuwar da ake kira Dow Jones sun fadi da kimanin maki dari hudu a cinikin da ake yi bayan da kasuwar ta tashi.


Kasuwannin hannayen jari suna ta tangal-tangal hagu da dama ainun cikin 'yan kwanai da suka wuce, sakamakon faragabar yaduwar tankiyar cinikayya tsakanin Beijing da Washington.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG