Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Yace Akwai Sauran Zabi


GOP 2016 Convention

Shugaban Amurka Donald Trump yace akwai sauran lokaci kafin ayi tunanen daukar matakin da ake jin ya dace game da kasar Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump yace “sai da mu tsaya mu jira, mu gani tukuna, amma dai ba wannan ne zabinmu na farko ba.”

Shugaban yana maida amsa ne ga tambayar da aka yi mishi na cewa ko yana shirin daukar matakin soja na yakar Koriya ta Arewa (KTA).

Shugaban dai yana kalamin ne a fadarsa ta White House jiya jim kadan bayan wata tattaunawar wayar tarho da yayi da shugaban kasar China, Xi Jinping.

Lokacinda wakilan VOA suka tambaye shi abin da suka tattauna da shugaban kasar ta Sin, Trump yace shugaba Xi yana son yin wani abu kan China, sai dai bai fayyace ko mine ne abin ba.

Duk da haka shugaban Amurka din yace shi da shugaban China, ra’ayinsu kan KTA ya zo daya “100 bisa 100.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG