Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Yayi Tur Da Hari Da Makamai Masu Guba a Syria


Yara da hari da makamai masu guba ya shafa bayan mutuwan mutane fiye da 40
Yara da hari da makamai masu guba ya shafa bayan mutuwan mutane fiye da 40

Shugaban Amurka Trump ya sha alwashin mayar da martani akan harin da aka kai da makamai masu guda cikin sa'o'i 48 bayan wata muhimmiyar shawara da zai yi

A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump yayi tir da mummunar harin rashin imani da aka kai da makamai masu guba a kasar Syria, yana mai cewar nan da sa’o’I 24 zuwa 48 zai yanke "muhimmiyar shawara" a kan martanin da Amurka zata dauka akan harin.


Trump ya fadawa hukumar majalisar ministocinsa a wata ganawa da suka yi a fadar White House cewa, Amurka zata bi diddigi ta gano wanda ya kai harin, ko Syria ce ko Rasha ko Iran ko kuma dukkanin su.


Tun da fari, sakataren tsaro Jim Mattis, yace Amurka tana nazarin daukar matakin soji a kan Syria, bayan da Trump ya aike da sakon tweeter a kan cewa za a ga "babban matakin ladabtarwa" kan duk wanda ya kai wannan harin rashin Imani da makamai masu guba, a yankin dake hannun yan tawaye dake kauyen Damascus, harakalla mutane 40 suka halaka a ranar Asabar.

Syria dai ta musanta cewa ta yi amfani da makamai masu guba a duk tsaawon lokacin rikicin da aka fara tun a shekara ta 2011.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG