Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka zai fita yakin neman wa'adin shugabanci na biyu


Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama zai yi yakin neman a sake zabensa a jihar Ohio a wunin yau laraba , inda ake sa ran zai kare manufofin tattalin arziki da gwamnatinsa ta sa a gaba wadda ke samun zazzafar suka, a dai dai lokacin da yakin neman zabe na bana yake kara kan-kama.

Shugaban Amurka Barack Obama zai yi yakin neman sake zabensa a jihar Ohio a wunin yau laraba , inda ake sa ran zai kare manufofin tattalin arziki da gwamnatinsa ta sa a gaba wadda ke samun zazzafar suka, a dai dai lokacin da yakin neman zabe na bana yake kara kan-kama.

Mr. Obama zai fita yakin neman zabensa na farko cikin wan nan shekara zuwa jihar wacce tilas ne shugaban kasan ya sami nasara cikinta idan har zai sake lashe zabe. A dai dai lokacin da aka fi maida hankali kan zaben fidda dan takara na jam’iyyar Republican, shugaban na Amurka zaiyi jawabi a wata makaranatar sakandare a yau laraba.

Fadar White House bata bada cikakken bayani kan ziyarar ta shugaban na Amurka ba, sai dai ana jin Mr. Obama zai maida hanklai ne kan sake farfado da tattalin arzikin Amurka da samar da ayyukan yi, lamari da fadar shugaban na Amurka take zargi wakilan majalisa ‘yan Republican sunki muhawara akai.

A jiya talata shugaban na Amurka ya kaddamar da yakin neman a sake zabensa lokacin da yayi jawabi ga magoya bayansa a Iowa kai tsaye ta vidiyo daga a zaben ‘yar tinken da aka yi a jihar. A jiyan ne duka manyan jam’iyun siyasar na Amurka suka kaddamar zaben fidda dan takara a zaben shugaban kasa da za a cikin watan Nuwamban bana.

Da yake magana daga Washington Mr. Obama ya bayyana irin nasarori da gwamnatins a ta samun da suka hada da garambawul kan harkokin hada-hadar kudi a kasuwannin sayar da hannayen jari da kuma na inshoran kiwon lafiya, kawo karshen yakin Iraqi, da kuma cire dokar da ta hana ‘yan luwadi da madugo aikin soja idan suka bayyana irin wadanda suke sha’awar tarawa dasu.

XS
SM
MD
LG