Shugaban Amurka Donald Trump jiya Jumaa cikin hushi yasa hannu ga dokar data bada damar kashe kudi dala tiriliyan daya da digo 3.
Yayi hakan ne ko bayan an dauki tsawon sao’I, cewa za a hau kujerar naki domin ko hakan bai kare bakin hauren nan da aka shigo dasu Amurka ba tun suna kanana, ko kuma yunkurin sa na gina Katanga a bakin iyaka.
A wani taron gaggawa na manema labarai da aka shirya a jiya Jumaa a fadar White House, Trump ya shaidawa manema labarai cewa ya dai sawa wannan dokar hannu ne kawai domin ganin hakan zai inganta matakan tsaro duk da cewa bai ji dadin abubuwa da dama dake kunshe cikin wannan Dakar ba.
‘’Yace bazan kara sawa wata doka irin wannann hannu ba’’ “Yace bama fa wanda ya karanta dokar wadda take sa’a daya Kenan da samar da ita, wasu mutane ma basu san cewa wannan adadin kudin shine irin san a biyu mafi girma da aka taba samarwa.
Sawa wannan dokar hannun dai ya kawar da kulle ayyukan gwamanatin tarayya a daren jiya jumaa.
Trump yaci gaba da shaidawa ma manema labarai cewa gaskiya ya duba dinbin tasirin kujerar nakin nan ne yasa har yasa ma wannan dokar hannu, kana kuma ayyukan soja zasu bunkasa kwarai da gaske.
Yace wannan matakin zai sa ayyukan sojan Amurka ya kankama tare da samun Karin biya har na wani lokaci mai tsawo.
Haka kuma ya kara adadin kudin da maaikatar tsaro zata kashe da wurin dala biliyan 60 daga shekar 2017.
Gaba daya dai dokar ta bada damar adadin kudin maaikatar tsaro yakai har dala biliyan dari 7, wanda wannan shine mafi girma a cikin shekaru 15 da suka gabata.
Facebook Forum