Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Boko Haram Ya Yiwa Gwamnatin Najeriya Wakin Bargo a Wani Sabon Bidiyo


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

A wani sabon faifan bidiyo da Abubakar Shekau , shugaban Kungiyar Boko Haram, ya fitar jiya, ya kalubali gwamnatin shugaba Buhari da shugabancin sojojin Najeriya tare da yi masu wankin bargo na cewa suna nan daram kuma zasu cimma muradunsu na kafa daular Islama bisa akidarsu

A cikin sabon faifan bidiyon da ya fitar mai tsawon mintuna talatin da shida da 'yan kai, madugun kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya yiwa gwamnatin Najeriya da tsarin dimokradiya wakin babban bargo.

Ya jaddada cewa har yanzu yana nan a raye kuma cikin koshin lafiya a daularsu. Abubakar Shekau ya ambato wasu shugabannin siyasa da na jami'an tsaro tare da fada masu suna nan kan bakarsu na cimma muradunsu na kafa daular Islama ta akidarsu.

A kan ma'anar wannan sabon faifan tsohon jami'in leken asirin sojojin Najeriya Aliko El-Rashid Harun yana mai cewa ya fitar da bidiyon ne ya nunawa mutanen Najeriya da duniya cewa sunan nan daram kuma duk wani ikirarin da sojojin Najeriya ke yi ba zai kawo masu illa ba. Yace a lura bayan da Mukaddashin shugaban kasa ya ce hafsan sojoji su koma Borno, kungiyar ta kara kai hare hare har sau talatin kawo yanzu. Hare haren sun fi na baya.

Dangane da cewa ko wannan bidiyon farfaganda ne Aliko ya ce ba zai zama hakan ba saboda a cikin wannan watan sun fitar da bidiyo biyu.

Kwararru irin su Baba Yola Muhammad Chango na ganin lokaci ya yi da za'a tura dokacin dakarun Najeriya zuwa dajin Sambisa da zagayen tafkin Chadi domin yin "gumurzun a yita ta kare". Yana mai cewa tsoron a rutsa da fararen hula idan an tura sojoji dajin Sambisa, sai ya ce " ai ko yanzun ma basu tsira" saboda haka kamata yayi a yita ta kare.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG