Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Falasdinawa Ya Kira A Yi Babban Taro Kan Gabas ta Tsakiya


Shugaban Falesdinawa, Mahmud Abbas

A zauren kwamitin slhun Majalisar Dinkin Duniya shugaban Falesdinawa ya yi wani dogon jawabi inda ya kira a yi babban taro akan Gabas ta Tsakiya domin a samu sulhun da zai ba al'ummarsa 'yancin yin walwala a yankinsu

Shugaban Falasdinu, Mahmoud Abbas, yayi kiran da a shirya wani taron kasa da kasa a kan zaman lafiya a tsakiyar wannan shekara, don kawo karshen daurin gwarman da aka samu a shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
Abbas ya fadawa taron wata-wata na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, kan batun rikicin Isra'ila da Falasdinawa cewa, "cijewar shirin zaman lafiyar da muke fuskanta, ba zai sa mu ja da baya ko mu karaya ba."

Shugaban na Falasdinawa, ya bayyana goyon bayansa ga shirya babban taron da zai kara sanya hannun kasashen yankin da sauran kasashen duniya, kuma ya zayyana irin abubuwan da yake ganin ya kamata duk wani shirin zaman lafiya ya kunsa. Jawabin nasa shine na farko da Abbas ya yiwa wakilan kasashe goma sha biyar na kwamitin tun shekarar 2009.


Yace “a shirye muke mu fara tattaunawa nan da nan, domin samarwa al’ummarmu walwala da 'yancin cin gashin kai”.


Shugaban Falasdinawan yayi jawabin nasa ne a gaban zauren kwamitin da ya cika makil da jama’a a New York, inda aka dauki tsawon lokaci ana tafa masa. Abbas ya bar dakin taron nan da nan bayan ya kammala jawabinsa, ya ki sauraren jawaban wakilan Amurka da na Isra’ila da suka biyo bayan nashi.


Sai dai wakilin Isra’ila yayi amfani da wannan dama ya soki Abbas da gujewa jawabansu, kuma yace Abbas baya taimakawa magance matsala sai dai kara dagula al’amura.


Yace Abbas ya shigo ya bayyana bukatunsa kuma yayi tafiyarsa kuma “yana sa ran zaku tattauna ku fidda sakamako”, inji wakilin Isra’ila a kwamitin sulhun, Danny Danon, yace hakan bai yiwuwa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG