Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Da Amurka Ke Jagoranta a Syria Sun Mayar Da Martani


Jiragen dakarun Amurka samfurin F-15E Strike Eagles a sararin samaniya.
Jiragen dakarun Amurka samfurin F-15E Strike Eagles a sararin samaniya.

Rundunar gamayyar kasashen da Amurka ke jagoranta a rikicin Syria ta kai harin ramuwar gayya kan magoya bayan gwamnatin Syria.

Rundunar sojan Amurka ta ce jiragen saman yakin gamayyar kasashen da take wa jagoranci a yakin Syria sun hallaka mutane kamar 100 da rundunar ta ce magoya bayan gwamnatin Syria.

Dakarun sun ce sun kai farmakin ramuwar gayya ne akan dakarun gwamnati wadanda suka kai hari haka siddan akan mayakan SDF da Amurka ke goya wa baya.

Ana ganin wannan harin da su mayakan SDF suka kai kamar wani yunkuri ne na sake kwato wasu yankunan da suka kwace daga hannun mayakan ISIS a cikin watan Satumbar da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG