Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ya Kamu Da Annobar COVID-19


Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron

An kara samun shugaban kasa da ya kamu da annobar Korona bairos.

Gwamanatin Faransa ta ce shugaban kasar Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona Bairos.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce “Shugaban kasa ya kamu da COVID-19 yau Alhamis” bayan da aka mai gwajin cutar “a lokacin da ya fara nuna alamunta.”

Gwamnati ta ce Macron zai killace kansa har na tsawon kwana 7, kamar yadda dokokin kasar suka tanada, kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida.

Shugaban na Faransa ya shiga jerin sunayen shugbannin kasashe da gwamnatoci a duniya wadanda suka kamu da COVID-19, cikinsu har da Firaiminstan Birtaniya Boris Johnson da kuma shugaban Amurka Donald Trump.

XS
SM
MD
LG