A yau Litinin, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, zai yi wa 'yan kasar jawabi kan zanga-zangar da ‘yan kasar da ake kira Yellow Vest ke jagoranta, wanda ya kai sati hudu yanzu.
Kafin jawabinsa, Macron na da niyyar zama da shugabanin kungiyoyi ‘yan majalisa, da manyan ‘yan kasuwa, domin tsara jawabi kan zanga-zangar da ke kawo tashin hankali a kasar.
Jiya Lahadi ma'aikata a Faransa sun share ragowan duwatsu, da motocin da aka kona, da kuma sauran barnar da aka aikata lokacin zanga zangar da ta kwashe makonni.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa yace shugaban Amurka Donald Trump, kar ya sa baki a lamarin siyasar Faransa, bayan da Trump ya yi rubuce rubuce kan batun a shafinsa na twitter.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 31, 2023
Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya
-
Janairu 30, 2023
Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan
-
Janairu 18, 2023
Mataimakin Shugaban Gambia, Badara Alieu Joof Ya Rasu A India
Facebook Forum