A karshen makon nan, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara wata ziyara a Jamhuriyar Nijar.
Dalilin wanna ziyara tasa shi ne domin ya gana da sojojin kasarsa da ke yaki da ‘yan ta'adda a Nijar.
Takwaran aikin sa Mahammadu Issoufou ne ya yi masa maraba da zuwa a babban birnin kasar na Niamey.
Shugabannin biyu za su gana domin tattaunawa akan sojojin Afirka da ke taka muhimmiyar rawa a yaki da ‘yan taadda.
Macron ya ce ba za su bar ‘yan ta'adda a yankin kasahen yankin Sahel da na sahara su ci gaba da tasiri ba.
Kasar Faransa wadda ta yi wa Jamhuriyar Nijar mulkin mallaka yanzu haka tana da dubban tsoffin sojojin girke a kasar.
Haka kuma Nijar din ce ta fi kowacce kasa yawan sojojin Faransa masu aikin samar da zaman lafiya.
Facebook Forum