Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Ya Nemi Hadin Kan Shugabannin Addinan Kasar


Shugaban Faransa Francois Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya tattauna da shuagabbnin addinai a yau Laraba a kokarin rage fargaba da ta biyo bayan wani dan ta’adda musulmida ya kashe wani limamin Katolika


Shugaba Hollande ya hada kan addinai da dama a ofishinsa a birnin Paris don tabbatar da hadin kai tsakanin addinan domin su tinkari hare haren ta’addanci dake kara ta’azzara a kasar Faransa.


‘Yan Katolika da dama ne suke ci gaba da bayyana razanansu a yau Laraba ganin kwana guda kenan da wani dan shekaru 19 da ake jira ayi shari’arsa da wasu da ba a ganosu ba suka kai wani hari cikin coci suka yanka wani limamin cocin mai shekaru 80 a lokacin da yake jagorantar ibada.

Harabar cocin da aka kai hari
Harabar cocin da aka kai hari


Sau biyu ne aka kama Adel Kermichie akan laifuka masu nasaba da ta’addanci tun cikin watan Maris na 2015.


Mahara biyu sun mutu yayayin da suka yi sa insa da ‘yan sanda, sai suka bude musu wuta suka kashesu.

Shugaban Musulmi na wannan yanki Mohammed Karabila, yayi wasu tambayoyi biyu yana cewa, ta yaya za ayi wanda ke sanye da mari ya kai wannan harin, sa’annan kuma ina ‘yan sanda suke har ya kai wannan hari.

Wasu daga cikin musulmi sun yi kira da a kara daukan matakan tsaro a masallatai, kuma sun yi kashedi da yan ta’adda masu bata sunan musulmin Faransa da na sauran nahiyar Turai baki daya.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG