Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Ya Ba Da Hakuri Kan Rushe Ginin Jakadancin Najeriya


Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta wayar tarho, inda ya bayar da hakuri kan rushe ginin ofishin jakadancin Najeriya da aka yi a Ghana.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar gwamnatin Najeriya mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnatin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.

A yayin wayar tasu, shugaban na Ghana ya fadawa Buhari cewa ya sa a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

A cewar sanarwar, da safiyar yau Talata ma, an kama wasu wadanda ake zargi da hannu a lamarin kuma za a gurfanar da su a gabatan kotu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG