Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo Addo, da sauran magabatan kasar sun halarci liyafar iftar, wato bude-baki, wadda Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Mahmud Bawumia, ya shirya albarkacin watan Ramadan.
Al’ummomin kasar Ghana, musamman ma na zango sun halarci wannan liyafa ta iftar wadda aka shirya a fadar gwamnati watau Jubilee House.
Tunda aka soma azumin wantan Ramadan Mataimakin Shugaban kasa ya soma rangadin jahohin kasar, ya na bude baki da al’ummomin Zango na jahohin, har lokacin da Allah ya kawo ranar yin iftar din a birnin Accra. Sauran magabatan da su ka hallara sun hada da Babban limamin kasa Shiekh Dr Usman Nuhu Sharubutu da Shugaban Majalisar sarakan zango, Sarkin Dagombawa Alhaji Abdul kadir Tahir da kusoshin gwamnati da kuma talakawa – musamman daga Zango.
Mataimakin Shugaban kasar ya yi farin ciki da haduwar dinbin jama’a, da su ka hada da Musulmi da wadanda ba Musulmi ba – musamman ma jami’an diflomasiyya, “Wannan lokaci ne na Ramadan, kamar yadda kuka sani wata
ne mai muhimanci wanda idan da roki Allah a cikinsa yak e amsawa da gaggawa.”
Sauran mutane ma sun tofa albarkacin bakinsu, ciki har da wanda y ace yayi farin cikin ganin yadda Musulmi da Kirista su ka hadu wuri guda - ciki har da Shugaban kasa – kuma ana cin abinci tare albarkacin watan Ramadan.
Ga dai wakilinmu a Ghana Ridwan Abbas da cikakken rahoton:
Facebook Forum