Shugaban babbar jam'iyyar Adawa ta kasar Zimbabwe, Movement for Democratic Change,(MDC), Morgan Tsvangirai, yace yana ganin lokaci yayi da zai koma gefe guda daga shugabancin jam'iyyar har ma da harkokin siyasa.
Tsvangirai dai shi ne shugaban jamiyyar ta MDC, tun kafa ta a shekarar 1999.
Tun daga wannan lokacin ake ta gwagwarmaya dashi musammam ma da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.
Shugaban ‘yan adawar dai yace zai sauka ne saboda girma ya kama shi kana yana fama da rashin lafiya.
Tun a cikin shekarar 2016 ne shugaban ‘yan adawar ya bayyana cewa yana fama da cutar sankara (cancer).
Sai dai a tattaunawar su da wakilin Muryar Amurka, James Butty, Farfesa Shaderick Guto na wata jami'a a Afirka ta Kudu yace dalilan yin murabus din na Tsvangirai ba zasu wuce dalilai biyu ba zuwa uku.
Yace na farko rashin lafiya kana na biyu shine sauka daga kan karagar mulki na tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sai kuma yadda jamiyyar ZANU-PF data sake sabon tsari wanda hakan zaiyi wahala ga jamiyyar ta MDC tayi wani tasiri a wani zabe a kasar nan gaba.
Facebook Forum