Accessibility links

Shugaban Kasa bai Amince Dala Miliyan Dubu Goma Sun Salwanta ba


Shugaban kasa Goodluck Jonathan
A firar da mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya Reuben Abatti yayi da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa yace shugaban bai amince dala miliyan dubu goma sun salwanta ba kamar yadda wasu kafofin labaru ke yayatawa.

Fadar gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta matuka gaya dangane da sababbin bayanai dake fitowa cewa wai shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya amince lallai dalar Amurka miliyan dubu goma sun salwanta daga asusun NNPC kamfanin da tun farko gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar Sanusi Lamido Sanusi ya yi zargin cewa wasu kudi sun bata. A zargin Sanusi yace kudaden basu shiga baitulmalin gwamnati ba kafin su fita kamar yadda doka ta tanada.

A lokacin da shugaban kasa ke ziyara a Amsterdam ya gana da 'yan Najeriya inda yace lallai ana zargin wasu kudade sun bata amma tuni an fara daukan matakai na tabbatar da abun da ya faru ba tare da wani cuwacuwa ba ko boyewa jama'a halin da ake ciki ba. Yace tun farko ana zargin batar miliyan dubu 49 ne, kana aka ce a'a miliyan dubu 20 ne kafin a ce miliyan dubu 12 ne. Yace duka da bincike-bincike tsakanin gwamnatin tarayya da kwamitin bincike na majalisa aka gano har yanzu akwai miliyan dubu 10 da ake kokarin a daidaita tsakanin masu binciken.

Inji Reuben Abatti wannan bayanin ba yana nufin shugaban kasar ya amince kudade sun salwanta ba ne. Yace a'a amma a wani lokaci can baya ma'aikatar kudi ta gwamnatin tarayya tace bata gama kammala daidaita miliyan dubu goma daga miliyan dubu ashirin da Sanusi Lamido Sanusi yayi zargin sun bata ba. Amma akwai matsaloli a NNPC kodayake ana kokarin gano abun dake boye. Yace shugaban kasa ya jaddadawa 'yan Najeiya a Amsterdam cewa gwamnatin kasar zata cigaba da tabbatar da gaskiya da adalci da kuma gudanar da mulki da dukiyoyin kasa a bude a daidai lokacin da zarge-zarge ke bazuwa. Yace tuni gwamnati ta amince a kawo kwararru kan bincike-bincike na kudade domin su gano gaskiyar abun dake faruwa.

Kodayake shugaban ya amince akwai matsala a kamfanin NNPC wannan ba yana nufin amincewa ne da zargin salwantar dala miliyan dubu goma ba. Reuben Abatti ya ba 'yan jarida shawara cewa su rika kwatanta gaskiya da tabbatar da bayani kafi a yayatashi domin kada a rudi jama'a ko a yiwa gwamnatin rashin adalci.

Gakarin bayani.
XS
SM
MD
LG