Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasa Ya Samu Sunayen Ministocin da Majalisa Ta Tantance


Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya mikawa shugaban kas Muhammad Buhari sunayen ministoci talatin da shida da majalisar ta tantance domin ya nadasu.

Bayan da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya mikawa shugaban kasa Muhammad Buhari sunayen ministocin da majalisar ta tantance, Shugaba Buhari ya yabawa majalisar da irin aikin da tayi.

Ya ba shugaban majalisar tabbacin cewa duk jihohin kasar talatin da shida zasu samu wakilci a majalisar zartaswarsa kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar ya tanada.

Sanata Shehu Sani ya bayyana irin rawar da majalisar ta taka inda yace an ba mara da kunya saboda adawar da PDP tayi na neman hana tantance wasu sunayen kamar Amaechi tsohon gwamnan Rivers. Sanata Sani yace sun yi abun da aka kyautata zato ba zasu iya ba.Yace sun nunawa duniya kawunansu a hade suke a karkashin shugabansu Bukola Saraki.

Da wannan nasar da shugaban kasa ya samu tare da jam'iyyarsa yanzu sai a sa ido a ga yadda zata kaya a harkokin mulkin kasar a karkashin shugaba Muhammad Buhari.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG