Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Burundi Ya Mutu


Shugaban Kasar Burundi, Pierre Nkurunziza

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya mutu sakamakon bugawar zuciya.

Wata sanarwar da gwamnatinsa ta fitar kan kafar sadarwa ta Twitter ce ta bayyana hakan.

Pierre dai yana da shekara 55 a lokacin da ya mutu.

Nkurunziza ya dade ya na fuskantar tuhume-tuhume kan abubuwan da su ka shafi yanayin siyasarsa tun lokacin da ya fara mulkin kasar a shekarar 2005.

Dama dai a watan Augustar wannan shekarar ne ya kamata ya ajiye mulki, ya mikawa janar Evariste Ndayishimiye mai ritaya wanda aka zaba a matsayin sabon Shugaba a cikin watan da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG