Accessibility links

Shugaban Kasar Kuriya Ta Arewa Kim Jong Il Ya Mutu

  • Halima Djimrao-Kane

Shugaba Kim Jong Il na kasar Kuriya ta Arewa wanda ya mutu ranar Asabar ya na da shekaru 69

Talbijin din gwamnatin kasar ya ce ya mutu ranar asabar sanadiyar gajiya

Talbijin din gwamnatin kasar Kuriya ta arewa ya bada labarin cewa shugaba Kim Jong Il ya mutu bayan shekaru 69 a duniya.

Wata mai karanta labarai a talbijin ta ce ya mutu a ranar Asabar sanadiyar gajiya. Wasu rahotanni sun ce ya mutu ne sanadiyar tsayawar zuciya, kuma a lokacin ya na balaguro a jirgin kasa.

Kim Jong Il ya kama mulki ne a shekarar 1994 bayan mutuwar mahaifin sa Kim Il Sung wanda ya kafa kasar Kuriya ta Arewa. Babu sahihin tarihin rayuwar Mr.Kim mai yawa. Ba kasafai ake ganin shi a bainar jama'a ba, kuma ba a cika saka muryar sa ta kafofin yada labarai ba.

Watakila a fi tuna shi a zama wanda ya bunkasa shirin nukiliyar kasar Kuriya ta Arewa, a yayin da miliyoyin 'yan kasar sa maza da mata ke mutuwa da yunwa.

A karshen shekarar da ta gabata Mr. Kim ya karawa dan autan sa Kim Jong Un matsayi ya ba shi mukamin janar mai taurari hudu, a cikin wani abun da aka fassara da cewa wani yunkuri ne na neman ganin dorewar gadon mulki daga uba zuwa da, a daular Kwaminisancin wadda ita kadai ce irin ta a duk fadin duniya

Masu fashin bakin al'amura sun ce a tsaya a gani ko za a samu jayayyar neman shugabanci tsakanin manyan janar-janar din sojin kasar ko kuma da zai gaji uban sa cikin ruwan sanyi.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG