Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amirka sun fice daga Iraq


Sojojin Amirka na rundunar Calvary a lokacinda suka isa kasar Kuwait
Sojojin Amirka na rundunar Calvary a lokacinda suka isa kasar Kuwait

Jerin gwanon motocin sojojin Amirka na karshe sun bar Iraq, sun shiga Kuwaita a yau Lahadi.

Jerin gwanon motocin da suke jigilar sojojin Amirka na karshe sun bar Iraq, sun shiga Kuwaita a yau Lahadi.

Da misalin karfe bakwai da mitocin talatin da takwas na safe agogon can jerin gwanon motocin da suke jigilar sojojin suka tsalaka kan iyaka, suka bar yan daruruwan sojojin Amirka a ofishin jakadancin Amirka a birnin Bagadaza.

Sojojin sun janye bayan fafatawar kusan shekaru tara, kimamin sojojin Amirka dubu hudu da dari biyar da dubban yan kasar Iraq aka kashe a yakin.

A shekara ta dubu biyu da uku aka fara wannan yaki da burin hambarar da gwamnati Saddam Hussein. A lokacinda ake ganiyar fafatawar fiye da sojojin Amirka dubu dari da saba’in aka girka a sansanoni fiye da dari biyar a Iraq.

Ya zuwa jiya asabar kuwa, kasa da sojoji dari uku ne aka bari a Iraq. Masu la’anar wannan yaki, sun caccaki Amirka da laifin barin kasar da aka yi wa kaca kaca, dubban mata an kashe musu mazaje a yayinda kuma ga dubban marayu, sa’anan kuma kawunan yan kasar na rarrabe ba tare da gyara wasu abubuwa ba. Shugaban Amirka Barack Obama yace makomar kasar tana hannun yan kasar.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG