Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kungiyar Samar da Agajin Gaggawa Ta Duniya ICRC Ya Kai Ziyara Borno


Peter Maurer shugaban ICRC na Duniya

Shugaban Kungiyar Samarda Agajin Gaggawa ko ICRC ya kai ziyara jihar Borno inda ya jajantawa wadanda aka jefa masu bam bisa kuskure a garin Rann

Shugaban ya nuna damuwarsa bisa ga kuskuren da mayakan saman Najeriya suka yi wanda ya kai ga hallaka mutanen da suke gudun hijira da ma'aiktan jinya.

Cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ma'aikatan jinya na kungiyar sa kai da ake kira Doctors without Boarders su guda shida. Ya yi masu addu'ar neman gafara daga Ubangiji.

A cewarsa su a ICRC suna bakin ciki da aukuwar lamarin suna kuma yin addu'ar cewa irin wannan kuskuren ba zai kara aukuwa nan gaba ba ganin cewa wadanan mutane ne da suka sadakar da rayukansu kuma sunyi aiki tsakaninsu da Allah domin taimakawa 'yanuwansu mutane da suka samu kansu cikin halin kakanikayi..

Tawagar kungiyar ta ziyarci asibitin kwararru dake Maiduguri inda nan ma suka jajantawa wadanda bala'in ya shafa. Baicin yi masu jaje sun bada tallafin kayan abinci.

Dr. Bulama Mari Gubio shi ne mataimakin kungiyar Red Cross ta jihar Borno kuma shi ne sakataren dattawan jihar yace idan Allah Ya yadda iyalan wadanda suka rasa rayukansu ba zasu yi rayuwa cikin bakin ciki ba. Gwamnati na shirya masu tallafi haka ma hukumomin SEMA da NEMA suna nasu kokarin. Akwai wasu alkawuran da aka kuma yi.

Wadanda aka taimakawa sun gode tare da yin addu'ar Allah Ya saka masu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG