Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kungiyar Taliban Yace Amurka Zata Yi Babban Kuskure Idan Ta Kara Yawan Sojojinta AaKasar


 Mayakan Taliban a lardin Shindand dake Yankin Herat, Afghanistan.
Mayakan Taliban a lardin Shindand dake Yankin Herat, Afghanistan.

Maulavi Haibatullah Akhunzadah, yayi gargadi kan cewa sojojin Amurka ba zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya ba sai dai su ‘kara rikita lamarin.

Shugaban kungiyar Taliban ya ce Amurka zata yi babban kuskure idan ta ‘kara yawan sojojinta a kasar ta Afghanistan don ta yaki mayakanta, wadanda suka lashi takobin cewa ba zasu taba daina fafutika ba sai ranar da suka ga bayan daukacin dukkan sojojin kasashen ketare dake kasar.

Maulavi Haibatullah Akhunzadah, ya yi wannan kalaman ne a yau Juma’a, a wani sako da ya fitar kafin shagalin Sallah da za’ayi a karshen watan Azumin Ramadan.

Yace “Idan kuna tunanin zaku ‘karya lagonmu kasancewar kun zuba sojoji masu yawa, kuna yin kuskure! Wannan ba ita bace hanyar warware matsalar ba.”

Shugaban ya kuma yi gargadi kan cewa sojojin Amurka ba zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya ba sai dai su ‘kara rikita lamarin'.

Ya kuma ci gaba inda ya zargi sojojin ‘kasashen waje da laifin hana ruwa gudu a kokarin samar da zaman lafiya a Afghanistan. Taliban tana bukatar sojojin kungiyar tsaro ta NATO su bar ‘kasar kafin ta amince da wani zaman tattaunawa.

A kwanan nan ne shugaba Donald Trump, ya amincewa sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, ya ‘kara aika dubban sojoji zuwa Afghanistan kan 8,400 da ake da su yanzu haka. Aikinsu shine horarwa da kuma baiwa dakarun ‘kasar shawara, wadanda ke fama wajen shawo kan kungiyar Taliban.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG