Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ma'aikatar Leken Asirin Amurka Ya Yi Murabus


Dan Coats
Dan Coats

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa shugaban ma’aikatar leken asiri ta kasa Dan Coats ya yi murabus bayan ya kwashe shekaru biyu a kan aiki kana yana aiwatar da shirye shirye masu cin karo da manufofin White House.

Wani sakon twitter da Trump ya fitar jiya Lahadi na cewa Coat zai ajiye aiki a ranar 15 ga watan Agusta, Ya godewa Coats da aiki da ya yiwa kasar. Shugaban yace zai nada dan majalisa na Republican daga jihar Texas kuma mai biyayya ga Trump John Ratcliffe ya maye gurbin Coats.

Trump ya kwatanta Ratcliffe a matsayin mai mutunci, tsohon Antoni janar na Amurka, wanda keda kwarewar da zai yi kyakkyawan jagoranci da kuma zaburar da kasar da yake matukar kaunarta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG